AHMAD CINEMATIC :
Naji daɗin raddinda Alhaji Ɗan Gaske yayyiwa Shehu Baye Mansur Kaduna, yayinda duk mai hankali zai fahimci cewa musayar yawunda aka samu tsakaninsu ɗan gaske ne kan daidai.✍️🥰
Shehu Baye Mansur Kaduna, ya miƙe ne yayiwa Ɗan gaske raddi, raddinda yake ɗauke da fuska biyu✌️FUSKA TA ƊAYA: maganar Shehu Baye Mansur Kaduna ga Ɗan Gaske, yayita ne dalilin ɗan gaske na haɗuwa da MAƘI¥AN SHEHU IBRAHIM NIASS KO MAƘI¥AN SHEHU AHMAD TIJJANI R.T.A, Shi kuma Alh. Ɗan Gaske dalilinsa na karɓa kowa hannu biyu-biyu shine indai kai masoyin Annabi ne bazai gujeka ba, inda ba ƙiyayyar Annabi kakeyi ba bayyananniya to bazai ƙyamaceka ba, saboda haka ya yarda ya haɗu da kowa akan Annabi Muhammad, wanda wannan shine daidai.
FUSKA TA BIYU: maganar Shehu Baye Mansur Kaduna ga Alh. Ɗan Gaske, yayita ne dalilin a zatonsa mabiyansu da suke fahimta ɗaya dashi suna zuwa wajen, Alh. Ɗan Gaske ne domin kuɗi ne, duk da taronsa yana haɗawa da waɗanda suke da saɓani ta fahimta dasu, Amman saboda kuɗi suke jurewa fushinsu na maƙiyansu suke zuwa wajen, wanda a ta'arifin maganar Baye Mansur yana nuni da cewa to su ba waɗannan marasa zuciyar bane da kuɗi zasu dinga kaisu wajenda ake wulaƙantasu (Haɗuwar Ƴan Izala waje ɗaya da Ɗan Gasken ana sukar Ƴan Ɗariƙa)
TANBIHI: Ni a mahangata ɗan gaske na akan daidai yana kan turba ta gaskiya, hujjata ita ce: “Idan soyayyar Annabi ce to ka yarda ku haɗu da kowa indai ba maƙiyin Annabi bane, amman akan Annabi kuyi baran-baran da kowa kowaye.”
To nidai banga laifin hakan ba, domin shi Alh. ɗan gaske duk masoyan Annabi nasa ne, bal dai nasan cikin waɗannan fahimtocin, Ɗariƙa ko Izala duk wanda suka haɗu dashi a wani MAJALISI to yana nuna yafi sonsu akan ɗayan ɓangaren wannan kuma ba wani abu bane na aibu face dattako da iya mu’amula da jama’ah.
Kayarda ku haɗu da kowa akan Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi, Amman akan saɓanin haka kuyi baran-baran da kowa kowaye komai matsayinsa.
Ahmad Bello ✍️✍️
2026-10-26 18:07:45